An yi kira da ɗaukar tsauraran matakai kan ´yan ƙungiyar PKK
November 3, 2007Talla
A lokacin da yake magana a gun babban taron kasa da kasa a birnin Istanbul akan halin da ake ciki a Iraqi, FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan yayi kira da a dauki matakan gaggawa kan ´yan tawayen Kurdawa dake arewacin Iraqi. Ya ce samar da tsaro da kwanciyar hankali a Iraqi yana da muhimmanci ga kasar da kuma makwabtanta. Shi kuma FM Iraqi Nuri al-Maliki ya yiwa mahalartar taron alkawarin daukar matakan ba sani ba sabo a kan ´yan tawayen na kungiyar PKK. A lokacin da yake magana a gefen babban taron na birnin Istanbul kakakin gwamnatin Iraqi Ali al-Dabbagh ya ce a shirye gwamnatinsa ta ke ta kame shugabannin PKK dake arewacin Iraqi. Taron akan Iraqi na samun halarcin manyan wakilai na yankin da wakilan kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD da na kungiyar G8.