Maraba da korar jagoran sojojin duniya a Afirka ta Tsakiya
August 13, 2015Wasu kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun yi maraba da murabus din da shugaban tawagar wanzar da zaman lafiya na Majsalisar Dinkin Duniya a kasar Babacar Gaye ya yi bisa zarge-zargen aikata ta'asa da ake wa sojojin Majalisar.
Crepin Mboli-Goumba na wata kungiyar fafutukar kawo sauyi mai ma'ana a Afirka ya ce mutane sun kadu matuka dangane da rahotannin da ke kara bayyana na zargin da ake wa sojojin kiyaye zaman lafiyar na yin lalata da kanana yara.
Shi ma Gervais Lakosso na kawancen kungiyoyin fara hula fata ya yi cewa wannan murabus din zai bude kofar samar da sabon yanayin yarda da juna.
A ranar Laraba babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya sanar cewa shugaban rundunar zaman lafiyar ya amsa kiran da aka yi masa kuma ya mika takardar yin murabus.