Mace ta yi nasarar darewa kujerar shugabancin majalisar EU
January 18, 2022Talla
Majalisar dokokin tarayyar Turai ta zabi 'yar majalisar kasar Malta Roberta Metsola a matsayin shugaba a yayin wani zama da majalisar ta yi a yau Talata.
Nasarar da Metsola mai shekaru 43 ta samu na kuri'u 458 a cikin 616 bayan karawa da wasu takwarorinta mata, ta bata damar zama mace ta farko cikin shekaru da suka gabata da za ta shugabanci majalisar.
Wannan dai na zuwa ne bayan rasuwar tsohon shugaban majalisar David Sassoli. Roberta Metsola ta kasance guda daga cikin mambobin majalisar tun daga shekarar 2013. Dama tana gab da cika wa'adinta na shekaru biyar kafin ta kai ga wannan matsayin.