Za a tantanace wanda zai karbi mulkin Guinea Bissau
December 20, 2019A Guinea Bissau, 'yan takara da za su fafata a zagaye na biyu na zaben shuagaban kasa na ci gaba da yakin neman zabe domin bayyana manufofinsu da nufin samun goyan 'yan kasa a zaben 29 ga watan Disimba, inda za a fafata tsakanin Domingos Simoes Pereira na jam'iyya mai mulki da kuma Umaro Sissoko Embalo na bangaren adawa.
Shi dai Domingos Simoes Pereira na jam'iyyar PAIGC yana da manufofin ganin kawo karshen banbancin kabilanci da yanki da ake samu a kasar da ke yankin yammacin Afirka, kamar yadda ya nunar yayin yakin neman zabe, gami da bunkasa tattalin arzikin kasar da ke sahun gaba a jerin kasashen 'yan rabbana ka wadata mu.
Yayin da a daya bangaren Umaro Sissoko Embalo shi ma ya yi ikirarin magance matsalolin banbance-banbance da mutane ke nuna wa juna, da samar da ci gaba mai dorewa. Ranar 27 ga watan Disamba ake kawo karshen yakin nemai zaben, sannan jama'a za su kada kuri'a a zaben na 29 ga watan Disamba.