1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi bankin duniya da laifin gindaya sharuda wajen baiwa kasahe taimakon raya kasa--

Jamilu SaniSeptember 22, 2004

Kungiyoyin kare hakin bil adama na duniya sun zargi bankin duniya dalaifin yin brus da batun inganta muhali da kyautata jin dadin jama'a a harkokinsa na bada rance ga kasahe----

https://p.dw.com/p/BwVN
Hoto: dpa Zentralbild

Cikin wata takarda da daruruwan kungiyoyin kare hakin bil adama na duniya suka aikawa daractan baiwa kasahe bashi na bankin duniya Peter Woicke da kuma shugaban bankin duniya James Wolfensohn makon da ya gabata,sun zargi bankin duniya da laifin rashin yin sasauci wajen bada ranci na raya kasa ga wasu kasahe na duniya,tare kuma da rashin daukar matakan da suka dace na kare muhali ga alumomin da wasu aiyuka na raya kasahe suka shafi yankunan su.

Daractan baiwa kasahe rance na bakin duniya,Peter Woicke ya fito fili ya musanta zargin da kungiyoyin kare muhali na duniya ke yiwa bankin duniya kann yadda yake tsaurara manufofinsa na baiwa kasahe rance kudade na raya kasa,inda ya ce sashen da yake lura da shi ba baiwa kasahe talfin kudade na raya kasa na bakin kokarinsa wajen kyautata rayuwar aluma tare kuma da kare muhali,a dukanin manufofin da suke dauka bada bashi da harkokin da suka shafi zuba jari a bankin na duniya.

Jannke Bruil na kungiyar kare muhali ta Friends of the Earth International,ya baiyana cewar mutane masu hankali na iya fahimta yadda manufofin bakin duniya suka sa gaba a game da baiwa kasahe taimako na raya kasa,inda ya zargi bakin duniya da laifin gindayawa kasahe tsauraran sharuda kafin a basu taimakon kudade na raya kasa.

Da yake jawabi ga manema labaru daractan na hukumar baiwa kasahe rance na bankin duniya,ya tsara manufofinsa ne ta yadda hakan zai taimaka wajen cigaban kasahe amman ba tauye cigaban su ba.

Kalaman dai na Woicke sun zo ne a dai dai lokacin da hukumar baiwa kasahe ranci ta bankin duniya ta fitar da rahotanta na shekara,wanda kuma a cikinsa ta ce ta ware dola biliyan 4.75 a fanin zuba jari ga kamfanoni masu zaman kann su a kasahe masu tasowa na duniya,inda hakan ke nuni da cewar an sami kari kann irin kann irin kudaden da bakin na duniya ya ware a fanin zuba jari ga kamfanonin masu zaman kann su na kasahen masu tasowa da ya kai dola biliyan 3.85 a shekara ta 2003.

Kimanin dola biliyan 3.4 na wanan adadi na kudade bakin na duniya ya ware wajen bada rance na raya kasa ga kasahen duniya.

Tun bayan kafuwar bankin na duniya cikin shekara ta 1956,hukumar baiwa kasahe rance ta bankin duniya ta baiwa kasahe taimakon raya kasa na fiye da dola biliyan 44 daga cikin asusunta,yayin kuma da aka baiwa kasahe masu tasowa fiye da 140 na duniya taimakon raya kasa na dola biliyan 23.

Daractan hukumar bada rancin na bankin duniya,ya baiyana cewar hukumar su ta IFC ta rubanya irin kudaden da take bayarwa a matsayin taimako na raya kasa a wanan shekara ga kasahen Africa dake kudu da sahara,har ya zuwa kasahen tsakiyar Asia da wasu kasahe na nahiyar Turia ta yadda hakan zai taimaka wajen cigaban wadanan kasahe.