1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi jami'an tsaro a Kenya da cin zarafin farar hula

August 18, 2014

Kungiyar kare hakin Bil-Adama ta Human Rights Watch, ta fitar da rahoto kan yadda jami'an yaki da ta'addanci a Kenya ke kisan mutane a boye.

https://p.dw.com/p/1CwRT
Hoto: picture-alliance/dpa

Jami'an tsaron na rundunar yaki da ta'addanci, da ke samun kudaden tallafi daga Amirka, da kuma Birtaniya, na aikata laifukan kashe-kashen mutanen da suke zargi, ba tare da sun bi ta hannun shari'a ba. Kungiya ta yi kira ga kasashen da ke bayar da tallafin da su dakatar da bai wa wannan runduna tallafi.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta kare hakin Bil-Adama ta Human Rights Watch, ta ce tana da tabbacin wannan zargi nata cewa jami'an yaki da ta'addancin na Kenya na wuce gona da iri, wajen kashe-kashe da ma sace mutane. kana kuma suna batar da su ba tare da sanin inda suka shiga ba. Suna kuma kame mutanen da basu ji basu gani ba, sannan da mugunyar muzgunawa ga wadanda suke tsare. Kungiyar ta kara da cewa, wadannan miyagun ayyukan na jami'yan tsaro, ba su ne za su fitar da kasar ta Kenya daga kangi na ta'addanci ba.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal