1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi shugaban Ghana da karbar cin hanci

Gazali Abdou TasawaJune 23, 2016

Jam'iyyar adawar Ghana na NPP ta zargin shugaban kasar da karbar wata mota daga hannun manajan wani kamfanin kasar Burkina Faso da ya bai wa kwangilar aikin gina hanya.

https://p.dw.com/p/1JC0Z
John Dramani Mahama Präsident Amtseinführung Ghana
Hoto: Getty Images /AFP

A Ghana babbar jam'iyyar adawa ta NPP ta bukaci a gudanar da bincike kan wani cin hanci da ta ke zargin Shugaban kasar John Dramani Mahama da karbar cin hanci daga hannun kamfanin da ya bai wa kwangilar aikin gina wani titi da kuma katanga ta kewaye harabar ofishin jakadancin kasar ta Ghana a birnin Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Faso.Jam'iyyar adawar na zargin shugaban kasar da karbar wata mota daga hannun manajan kamfanin kasar ta Burkina Faso da ya bai wa kwangilar aikin gina hanya.

Sai dai shugaban kasar Ghanar ya yi watsi da wannan zargi wanda ya ce ba shi da tushe, hasali ma ya kalubalanci 'yan adawar da su yi amfani da damar da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su na kalubalantarsa a gaban kotu kan wannan zargi.

Gwamnatin kasar ta Ghana ta tabbatar da samun kyautar motar amma ta ce ba bu batun cin hanci a cikin lamarin, domin an saka motar ne a jerin motocin gwamnati ba wai mallakar shugaban kasar ba.