An zargi 'yan siyasar Iraki da hannu kan hali da kasar ke ciki
August 8, 2014Talla
Ayatollah Ali al-Sistani ya bayyana hakan ne a hudubar sallar Juma'a da ya gabatar a garin nan Karbala, in da a cikinta ya zargi 'yan siyasar Iraki da hannu a irin matsalolin da kasar ta fada, wanda ya ce shi ne mafi muni tun bayan da aka kifar da gwamntin Saddam Hussein.
Al-Sistani wanda ya ce rigingimun da ke faruwa sun samo asali ne sakamakon son kai da 'yan siyasa ke da shi, ya ja kunnen al'ummar Irakin da su hade kai su kuma tashi haikan wajen fuskantar kalubalen da ke gabansu.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaban Amirka Barack Obama ya ce gwamnatinsa za ta afkawa 'yan kungiyar ta IS muddin ta kai ga taba jami'anta da ma dai sansanoninta.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Suleiman Babayo