1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mutumin da ya kashe mabiyansan shafinsa na Twitter

Ramatu Garba Baba
December 15, 2020

Wata kotu a Japan ce ta zartas da hukuncin kisa kan Takahiro Shiraishi da aka samu da laifin halaka wasu masu bibiyar shafinsa na Twitter bayan yayi lalata da su.

https://p.dw.com/p/3mkVe
Japan Leichenfunde in Tokio
Hoto: Getty Images/AFP

Kotu a kasar Japan ta zartas da hukuncin kisa kan wani mutum da ya kashe mabiyansa a shafinsa na Twitter, Takahiro Shiraishi mai shekaru 30 da haihuwa, ya halaka mutanen tara ne bayan da yayi lalata da su. 

An gano yadda yake kitsa kisan ta hanyar jan hankulan matan bayan da suka baiyana masa damuwarsu na halin kuncin rayuwa da suke ciki, yana gaiyatarsu zuwa gidansa kuma bayan yayi lalata da su daga bisani ya kashesu ya kuma yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsu ya zubar. Mamatan sun hada da mata takwas da namiji guda, 'yan shekaru tsakanin goma sha biyar zuwa ashirin da shida da suka kasance masu bibiyan shafinsa.