Ana bukatar sabuwar koyarwar addini
February 23, 2015Babban limamin jami'ar Azhar ta kasar Masar Sheikh Ahmed al-Tayib ya fada wa wani babban taron yaki da ta'addanci a kasar Saudiyya cewa ya kamata a yi wa tsarin koyarwar addinin Musulunci garambawul. A jawabin bude taron a birnin Makka, Sheikh Ahmed al-Tayib ya yi nuni da cewa bisa tarihi akwai tarin kura-kurai na fassara cikin addinin da suka janyo tsauraran akidoji da ra'ayoyi tsakanin Musulmi. Yanzu haka dai manya-manyan malamai na ci gaba da taron na yini uku a Makka a kan yaki da ta'addanci a cikin addinin Musulunci. Sheikh Al-Tayib ya ce dole Musulmi su samu sabon hadin kai da zamanantar da koyarwar addini wanda kuma zai nuna karin juriya. Ya ce da haka ne kawai za a iya dakushe kyamar da ake nuna wa addinin Musuluncin a nahiyar Turai.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu