Ana ci gaba da nuna rashin amincewa da ci zarafin mata a Indiya
December 23, 2012Mahukuntan su ba da sanarwar aramta gudanar da zangazanga a kewayen gidan shugaban kasa da ginin majalisar dokoki. A jiya Asabar dubban mutane sun fantsama kan titunan domin nuna fushinsu. To amma 'yan sanda sun yi amfani da gas mai sa hawaye da feshin ruwa da kulake domin tarwatsa masu zangazanga da suka yi yunkurin rusa wasu shingaye da aka toshe hanyoyi da su. A yau Lahadi 'yan sanda sun harbi wata 'yar jarida a lokacin da ake gudanar da zanga-zanga.Tun wasu kwanaki da suka gabata ne dai ake gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da cin zarafin mata. Su dai masu zanga-zangar suna kira ne da a ba da kariya mai inganci ga mata a kuma tsananta hukunci akan wadanda ke cin zarafin mata. Kusan mako guda kenan da wasu maza shida suka ma wata daliba fyade a gaban abokanta a cikin bus a birnin New Delhi suka kuma ji mata ciwo da sandan karfe. A dai halin yanzu wannan yariya na kwance rai kwakwai mutu kwakwai a asibiti.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru- Danladi Aliyu