Ana ci gaba da tofa albarkacin baki game da rataye tsoffin jamian Iraq
January 15, 2007Kasashen duniya suna ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da rataye tsoffin jamian gwamnatin Iraq karkashin Saddam su biyu.
Kasashen Amurka da Burtaniya sunce anyi adalci ga wadannan mutane biyu,kodayake sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice tace babu mutunci hanyar da akabi ta kashe wadannan mutane.
Shi kuwa shugaban hukumar turai Jose Manuel Barroso yayi Allah wadai da hukuncin kisa da aka zartarwa tsoffin shugabannin na Iraqi.
Kasar Jordan makwabciya tace tana fatar wannan kisa ba zai kawo cikas ga shirin sulhu tsakanin alummomin Iraqin ba.
An dai rataye mutanen biyu ne da safiyar yau,makonni biyu bayan rataye tsohon shugaba Saddam hussein.
Rahotanni daga Bagadazan sunce kan danuwan Saddam Barzan Ibrahim Tikrit ya guntule daga jikinsa a lokacin ratayewar sai dai kuma kakakin gwamnatin Iraqi yace ba a keta hakin wadannan mutane ba.