Ana zaben 'yan majalisar dokoki na Turkiya
November 1, 2015Talla
Ana ci gaba da kada kuri'a a zabe kasa baki daya da ke wakana a kasar Turkiya, inda jam'iyya mai mulki ta AKP take fata kan samun kujerun majalisar dokoki da take bukata domin samun damar kafa gwamnati kai tsaye.
A zaben watan Yuni, kimanin watanni biyar da suka gabata, jam'iyyar Shugaba Recep Tayyip Erdogan mai mulki ta rasa rinjayen da take bukata a karo na farko cikin shekaru 13, abin da ya haifar da rashin iya kafa gwamnati, da ya janyo sake kiran zabe karo na biyu a shekara guda, a kasar mai mutane kimanin milyan 80. An jibge dubban jami'an tsaron musamman cikin yankunan Kurdawa na kasar ta Turkiya, saboda tabbatar da doka da oda.