Adadin wadanda suka rasu sun karu a Turkiyya da Siriya
February 13, 2023Talla
Turkiyya za ta kai karar wasu kamfanonin gine-ginen kasar da ta zarga da sakaci wajen kara ta'azzara mummunar girgizar kasar da ta yi mummunan illa.
Mataimakin shugaban Turkiyya Fuat Oktay, ya bayyana cewa akwai akalla kamfanoni 130 da ke shirin shiga komar mahukunta kan zarginsu da rashin samar da gine-gine mafi inganci a wurare da dama.
Ya zuwa wannan Litinin, akalla mutane dubu 35 ne suka rasu sakamakon tagwayen bala'o'in a Turkiyya da Siriya, adadin da kuma masu ceto ke ittifakin cewa ka iya karuwa nan da wasu lokutta.
Duk da debe tsammanin da ake na samun ragowar masu sauran numfashi, an ceto wasu mutane hudu a jiya Lahadi da ransu.