1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zambiya: Jana'izar Kenneth Kaunda

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 2, 2021

Shugabannin kasashen Afirka tare da al'ummar kasar Zambiya sun hallara a Lusaka babban birnin kasar, domin halartar jana'izar tsohon shugaban kasar marigayi Kenneth Kaunda.

https://p.dw.com/p/3vwW1
Kenneth Kaunda | ehemaliger Präsident Sambias
Marigayi tsohon shugaban kasar Zambiya Kenneth KaundaHoto: Alexander Joe/AFP/Getty Images

Marigayi  Kenneth Kaunda da ke zaman jagoran yakin kwatar 'yanci a Zambiya, ya kuma taimaka gaya wajen samun 'yancin kan kasashen Afirka da dama. Rahotanni sun nunar da cewa tuni shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa da takwaransa Emmerson Mnangagwa na Zimbabuwe suka isa Lusaka, domin girmama Kaunda ya rasu a ranar 17 ga watan Yunin da ya gabata yana da shekaru 97 a duniya. A shekara ta 1964 ne dai, Kaunda ya jagoranci samun 'yancin kan Zambiya daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, tare da marawa kungiyoyin masu rajin kishin kasa domin tabbatar da bayar da mulki ga al'ummar da ke da rinjaye a kasashen Angola da Mozambik da Namibiya da Afirka ta Kudu da kuma Zimbabuwe. Tuni dai shugaban kasar ta Zambiya Edgar Lungu ya isa babban filin wasa na Lusaka, inda za a gudanar da jana'izar Kaunda a hukumance.