1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMasar

Masar: Al'umma na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Abdourahamane Hassane
December 10, 2023

Al'ummar a kasar Masar na kada kuri'a a zaben shugaban kasa wanda yaƙin da ake yi a yankin zirin Gaza mai makwabtaka ya mamayeshi:

https://p.dw.com/p/4ZzLc
Abdel Fattah al-Sisi
Abdel Fattah al-Sisi Hoto: Egyptian Presidency Media Office via AP/picture alliance

 Kimanin masu kada kuri'a miliyan 67 ne ake sa ran za su je rumfunan zabe a ranakun Lahadi,da Litinin da Talata, kafin a a bayyana sakamakon  zaben a hukumance ranar 18 ga watan Disamba. Baya ga shugaban kasar mai barin gado, akwai yan takara guda ukku da ke fafatawa da shi, wadanda ake yi wa kallon jeka na hika.Bisa ga dukkan alamu shugaba mai ci, Abdel Fattah al-Sissi, yana da tabbacin lashe wa'adi na uku. Kasar Masar mai yawan al umma miliyan 106, na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni a tarihinta, wanda kashi biyu cikin uku na al'ummar kasar na  rayuwa cikin kangin talauci.