1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana murna da kisan gawurtaccin 'yan bindiga a Najeriya

Binta Aliyu Zurmi Abdoulaye Mamane
September 14, 2024

Hukumomi a Najeriya sun bayyana farin cikinsu da kisan da sojojin kasar suka yi wa wasu fitattun 'yan bindigar da ke addabar yankuna da dama na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4kd9m
Nigeria Bola Ahmed Tinubu
Hoto: Kola Sulaimon/AFP

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa dakarun sojan kasar bisa kisan gawurtaccen dan bindigar nan Halilu Sububu wanda ya addabi jihohin Arewa maso gabashin kasar, da kuma wani fitaccen dan bindigar daji Sani Wala Burki da jami'an Najeriya suka yi ikirarin kashewa a Katsina.

Karin Bayani : Sabbin matakan tsaro a Jihar Sokoton Najeriya

Fitaccen dan bindigar da ya yi kaurin suna a jihohin Sokoto da Zamfara, ya gamu da ajalinsa ne a yayin wani gumurzu tsakanin sojojin Najeriya a tsakiyar makon da ya gabata, inda sojojin suka tabbatar da hallaka shi tare da wasu manyan 'yan bindiga fiye da 40.

Jami'an tsaron Najeriya sun kwashe shekaru sun famar yaki da gungun mutane da ke satar al'umma da karfin bindiga domin neman kudin fansa.

Karin Bayani : Gwamnatin Najeriya na shirin daukar mataki a kan 'yan bindigar daji

Sojojin Najeriya sun sha alwashin magance matsalar 'yan bindigar daji, inda har ma babban hafsan hafsoshin Najeriya ya tabbatar da yunkurin sojan na kawo karshen Bello Turji guda daga cikin manyan barayin dajin da suka yi fice a arewacin Najeriya.

 Dan bindigar da aka kashe Halilu Sububu, ya jima yana hakar ma'adanai ta barauniyar hanya da sayar da bindigogi ga barayin daji da satar addabi al'umma a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Kaduna.