Hanyoyin neman mafita ga tattalin arzikin Jamus
November 5, 2024Jam'iyyun siyasa uku da ke cikin gwamnatin kawancen Jamus suna ci gaba da tattaunawa a wannan Talata, domin samun matsaya kan yadda za a samu manufofin tattalin arzikin kasar, abin da zai janyo hana rushewar gwamnatin kawancen, a daya daga cikin kasashe mafiya karfin tattalin arziki na duniya.
Karin Bayani: Volkswagen zai kori dubban ma'aikata
A wannan Laraba mai zuwa kuma za a ci gaba da tattaunawar tsakanin bangarorin a majalisar dokoki domin samar da kasafin kudin da duk bangarorin uku za su amince da shi, abin da ke zama gagarumin matakin ganin dorewar gwamnatin kawancen tsakanin jam'iyyar SPD mai matsakaicin ra'ayin gaba-dai gaba-dai, da jam'iyyar FDP mai ra'ayin jari hujja, da kuma jam'iyyar the Greens mai ra'ayin kare muhalli.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz na jam'iyyar SPD yana da fata kan cimma matsaya tsakanin jam'iyyun da ke cikin gwamnatin kawancen.