Ana shagulgulan jana'izar tsohon shugaban Koriya ta Arewa
December 29, 2011Daruruwan yan kasar Koriya ta arewa suka taru a dandalin tsakiyar babban birnin kasar Pyongyang a bikin jana'izar tsohon shugaban kasar Kim Jong Il. Dansa kuma magajinsa da sauran mayan hafsoshin sojin suka tsaya kan baranda, inda suke kallon yadda al'amura ke gudana. An dai watsa abin da ke faruwa kai tsaye daga gidan talabijin din Koriya ta arewa. Yau dai itace rana ta biyu da ake bikin jana'izar Kim Jong Il, wanda ya mutu sakamakon bugun zuciya a ranar 17 ga watan da muke ciki, kamar yadda hukumomi sanar. A shagugulan da ake yi ne dai aka bayyana dan marigayin Kim Jong Un a matsayin shugaban kasa, babban kwamandan askarawan kasar, kana jagoran jam'iyar komunisanci. An yi tsit na minti uku a dai-dai karfe 12 rana na kasar.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu