Duniya na Allah wadarai da kusten majalisa
January 9, 2023Da kyar da jibin goshi jami'an 'yan sanda suka kawar da masu boren da ke nuna adawa da samakon zaben kasar da ya ayyana Lula da Silva a matsayin zababben shuagaban kasa.
A gaban dandazon 'yan jarida a al'barkacin ziyarar aiki a Mexico, shugaban Amirka Joe Biden ya ce ya kadu kan yadda masu kutsen suka yi yinkurin karantsaye ga dandalin dimukuradiyya.
Su kuwa shugabannin kasashen China da Rasha da Canada da Italiya da Jamus, sun bi sahun sauran takwarorinsu na kasashen duniya wajen yin Allah wadarai da masu kusten, inda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya kara jaddada goyoyn bayansa ga zababben shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva.
A nashi bangare Fafaroma Francis, cewa yayi ya damu da irin nau'ukan tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa da ke faruwa a yankin Amirka, musamman ma na baya bayan nan da suka auku a Peru da Brazil.