Ana takaddama kan dokar kafofin zumunta a Najeriya
February 10, 2024Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa 'yan kasar ikon fadin albarkacin bakinsu da karfin gaske ko da kuwa ba dadi a kunnuwan 'yan mulki. Sai dai a idanun gwamnatin kasar, kafofin na sada zumunta sun rikide zuwa na tayar da hankali da bayyana labaran karyar da ke da illa ga rayuwa da makoma a cikin kasar.
Karin bayani: Najeriya: Kamen 'yar TikTok a jihar Kano
Ana Kallon kokarin na sada zumunta da zama kanwa uwar gamin a jerin rigingimu walau na siyasa ko addini a cikin Najeriya, ko bayan kokari na tayar da kayar bayan talakawa bisa batutuwa daban-daban.Abuja ta ce na zaman ummul aba'isan wata sabuwar dokar da yanzu haka ke shirin isa zauren majalisar wakilai ta kasar. Abbas Tajudden da ke zaman shugaban majalisar wakilai ta kasar ya ce dokar na shirin ingantar tsari na zumunta cikin kasar.
Karin bayani: Cin zarafi ta kafofin sadarwa na sada zumunta
Masu mulkin na kallon kokarin kafafen sada zumunta na iya rikidewa zuwa ga tayar da hankali da cin zarafi, yayin da masu sana'ar ta jarida ke cewa shirin na zaman wani yunkuri na rataye kare bisa laifin kura. Ana shirin yin dokar a lokacin da kafafen sadarwar ke dada tasiri a cikin sabuwar gwagwarmayar inganta rayuwa cikin Najeriya.
Karin bayani: INEC: Rawar masu amfani da kafafen sadarwa
Ya zuwa yanzu, wayoyi na zamani sun haifar da miliyoyin masu takama da kafofin sada zumuntar a wajen aike sako. Alhassan Yaya da ke zaman mataimakin shugaban kungiyar masu jarida ta kasar NUJ, ya ce suna shirin yin yaki da bukatar mahukuntan Najeriya. Ya zuwa farkon shekarar 2023, sama da mutane miliyan 31 ke amfani da kafafen sadarwa cikin Najeriya.