Ana zaben cike gurbin shugaban kasar Iran
June 28, 2024Rahotanni sun nuna yadda 'yan kasar suka fita zuwa rumfunan zaben cike gurbin marigayi shugaba Ebrahim Raisi, wanda ya kwanta dama a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu, makwanni biyar din da suka gabata, zaben da masharhanta ke dauka a matsayin kada kuri,ar raba gardama ga juyin juya halin musuluncin kasar.
Ta yiwu kiran da jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei ya yi musu kan su dauki fita wannan zaben a matsayin ci gaban gwagwarmayar tabbatar da adalci a kasa da ta da kayar baya ga manyan kasashen duniya, na daga cikin abin da ya karfafa masu zaben yin irin wannan fitar farin dangon, yadda kwanaki biyu a jere aka jiyo shi yana ta cewa:
"Ranar zabe a Iran, ranar farin ciki ce da murna, saboda tana alamta yadda ‘yan kasa suke kara jaddada mubaya‘arsu ga tsarin juyin juya halin Musulunci, duk da bambancin wadanda ke jagoransu a tsawan wa‘adin mulkin da ke sabuntuwa. Wannan kuma ita ce babbar alamar ‘yanci da sakin mara da ‘yan kasar nan ke da shi. Don haka nake fatan za ku yi tururuwar zuwa rumfunan zabe don nuna wa duniya irin amannar da kuka yi da wannan tsarin."
A ranar jajibirin zaben ne dai ‘yan takara biyu daga cikin masu ra‘ayin mazan jiya suka janye takararsu, lamarin da ya sanya a yanzu ‘yan takara hudu ne ke fafatawa da juna.
Kodayake, dan takarar masu matsakaicin ra‘ayi da ke rajin kawo sauyi, Mas‘oud Pezeshkiyan wanda tsoffin shuwagabanin kasar Hassan Rouhany da Muhammad Khatamy ke mara wa baya, ya yi watsi da kuri‘ar jin ra‘ayin jama‘ar, yana mai amannar cewa, muddin ‘yan kasar da ke neman sauyi za su fita zabe, to zai bai wa marada kunya.
Hukumar zaben kasar dai ta ce kimanin ‘yan kasar miliyan 61 ne suka cancanci kada kuri‘a. An fara kada kuri'a a rumfunan zabe 58,640 a fadin kasar ta Iran, akasari a makarantu da masallatai.
Ana sa ran hasashen sakamako da wuri a safiyar ranar Asabar da kuma sakamakon hukuma a ranar Lahadi. Idan babu cikakken rinjaye bayan kuri'ar ranar Juma'a, ‘yan takara biyu na farko za su fuskanci zagaye na biyu na zaben ranar 5 ga watan Yuli. Wanda ya yi nasara zai yi shekaru hudu kan karagar mulki.