1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zargin Amirka da take hakkin dan Adam

January 19, 2006

Kungiyar Human Rights Watch ta buga rahotonta na shekara-shekara, inda ta yi kakkausar suka ga gwamnatin shugaba Bush da take hakkin dan Adam, musamman ma dai dangane da fursunonin da dakarun Amirkan ke tsare da su a sansanoni daban-daban, wai don yakan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/Bu2H
Fursunoni a sansanin Guantanamo Bay
Fursunoni a sansanin Guantanamo BayHoto: AP

Kungiyar Human Rights Watch dai, tana kula da manufar kare hakkin dan Adam ne a fiye da kasashe 70 na duniya. A cikin rahotonta na wannan shekarar dai, ta yi kakkausar suka ne ga gwamnatin shugaba Bush na Amirka. Bisa ganin kungiyar dai, gallaza wa fursunoni da kuma azabtad da su, wato ba wata kaucewa daga ka’idoji ne da wasu sojojin kasar dai-dai suke yi ba. Wata manufar siyasa ce da gwamnatin Amirkan ta sanya a gaba, a fafutukar da take yi, wai ta yakan ta’addanci. Da yake gabatad da rahoton, darektan Kungiyar ta Human Rights Watch, Kenneth Roth, ya bayyana cewa:-

„Wulakantad da fursunoni da azabtad da su na cikin manufofin siyasar Amirka. Akwai dai wasu kasashe kuma, da ke gallaza wa fursunoni, inda ma lamarin ya fi muni. Amma suna yin hakan ne a asirce. Amirka, ita ce farkon kasa a duniya, wadda ta fito fili a shekarar bara, ta bayyana a hukumance cewa tana da `yancin daukan tsauraran matakai kann fursunonin.“

Ita dai kungiyar, tana hujjanta zargin da take yi wa gwamnatin Amirkan ne da jawaban da manyan jami’anta suka sha yi a kan wannan batun, da kuma barazanar hawan kujerar na ki da shugaba Bush ya yi, wato na kin sanya hannu kan wani kundin dokar hana gallaza wa fursunoni da majalisar dattijan kasar ta tsara. Wadannan matakan da gwamnatin shugaba Bush ke dauka dai, sun saba wa dokokin kasar, kuma ba sa ma haifad da wani kyakyawan sakamako, inji kungiyar. A daura da haka ma, tana kara angaza masu tsatsaurar ra’ayi su dinga yada akidarsu, suna kuma janyo hankullan matasa, wadanda su ma ke iya zamowa `yan ta’adda. Bugu da kari kuma, matakan na janyo rashin amincewar jama’a da manufofin gwamnatin ta shugaba Bush. Ana kuma ta kara samun yawan fursunonin da aka tsare, ba tare da an sami wani dalili na gabatad da su gaban shari’a ba. Sakamakon da matakin gwa,mnatin Amirkan zai iya janyowa dai shi ne, inji Roth:-

„Yin kwaikwayo ko kuma matashiya da Amirka da sauran kasashe za su iya yi. Hakan kuma zai gurgunta matsayin da Amirkan ke da shi a duniya na kasancewa mai kare hakkin bil’Adama a fagen siyasar kasa da kasa.“

Kungiyar ta Human Rights Watch, ta yi kira ga nada wani alkali mai zaman kansa, wanda kuma ba shi da jibinta da duk wasu kafofin siyasa, don ya gudanad da bincike kan take hakkin bil’Adama da Amirka ke ta kara yi. Har ila yau dai, kungiyar ta kuma yi kakkausar suka ga gwamnatin Rasha. Ban da dai gallaza wa al’umman Checheniya, ana zargin mahukuntan fadar Kremlin ne da tafiyad da wata siyasar danniya a sauran yankuna na kasar. A kan wannan zargin dai, Roth ya bayyana cewa:-

„Shugaba Putin dai ya karfafa matsayinsa ne ta hanyar yi wa bangarorin kasar masu zaman kansu danniya. Ana iya ganin hakan ne a zahiri a majalisar kasar, ko kuma Duma, da salon nada gwamnoni da shugaban ke bi da kuma take hakkin maneman labarai da hana su gudanad da aikinsu kamar yadda ya kamata.“

A karshe dai, kungiyar ta Human Rights Watch, ta ce an sami munanan cin amanar jama’a da take hakkinsu a kasashen Bama, da Korea ta Arewa, da Turkmenistan, da Tibet da kuma jihar Xinjiang ta kasar Sin. Ta kuma ambaci batun ta da dimbin yawan jama’a daga matsugunansu saboda dallilan siyasa a kasar Zimbabwe.