Ancimma yarjejeniya kan nuclearn koriya ta arewa
February 13, 2007Wakilan kasashe shida dake halartan taron warware rikicin nuclearn kasar Korea ta arewa sun cimma yarjejeniya,wanda ke zama karon farko da aka samu daidaituwa bayan shekaru uku a ana tabka mahawarar data kasa haifar da wani tudun dafawa a dangane da wannan rikici.Wakilin Amurka a wajen taron kuma mataimakin sakatariyar harkokin wajen kasar Christopher Hill,ya fito daga zauren taron da safiyar yau bayan tattaunawar saoi 16,inda ya sanar dacewa an cimma yarjejeniya tsaakanin bangarorin da koriya ta arewan.Yarjejeniyar dai ta kunshi alkawuran dakatar da sarrafa makamai da kuma tallafin samarda makamashi.Anasaran kafa kungiyoyi wadanda zasuyi aiki domin shawo kann matsaloli na sabadi da kasashen yankunan ke fuskanta da juna.To sai dai koriya ta arewan batace komai ba.Ayayinda koriya ta kudu ta bayyana cewa ,yarjejeniyar na neman amincewar gwamnatocin dukkan wakilan kasashen dake halartan wannan taron kafin ta fara aiki.