Anfani da makamai masu guba a kan fararen hula a Siriya
August 19, 2013Sifetocin na Majjalisar Dinkin Duniya za su yi kokarin gano ko bangarorin da ke yaki da junansu a kasar sun yi anfani da makamai masu guba. Ayarin da ya kunshi kwararru 20 daga Majalisar Dinkin Duniyar dai, ya isa Damascus, fadar gwamnatin kasar ta Siriya ne a wannan Lahadin, bayan da majalisar ta cimma yarjejeniya tare da gwamnatin Siriya, wadda ta bata damar gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru dangane da zargin yin anfani da makamai masu gubar, bayan tsawon watannin da sassan biyu suka yi sua takaddama a kan batun.
Hukumomin kasar ta Siriya dai, sun baiwa tawagar masu binciken damar kai ziyara a wasu wurare uku, domin tantance ko an yi anfani da makamai masu guba a yakin basasar kasar, amma ba wai don gano bangaren da ke da alhakin yin anfani da makaman ba wajen kaddamar da hare hare.
Tawagar, wadda ke karkashin jagorancin kwararre a sha'anin makamai daga kasar Sweden, wato Aake Sellstroem, ana sa ran za ta tantance yiwuwar yin anfani da makaman ne a Khan al-Assal, da ke kusa da birnin Aleppo. Gwamnatin Siriya ta zargi 'yan tawaye da yin anfani da makamai masu guba a ranar 16 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 26, cikinsu kuwa harda da dakarun Siriya 16, amma kuma su ma 'yan tawayen suka ce gwamnatin ce ke da alhakin kaddamar da harin. Sauran wurare biyun kuwa na kusa da birnin Damascus ne, da kuma wani dake kusa da birnin Homs.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal