Anfani da makamai masu guba a yakin Siriya
August 22, 2013Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya yayi kira ga gudanar da cikakken bincike dangane da zargin cewar, sojojin kasar Siriya sun yi anfani da makamai masu guba, yayin wani hari da suka kaddamar a kusa da Damascus, babban birnin kasar. 'Yan dawar Siriya sun zargi dakarun gwamnatin da harba makamai masu linzamin da ke dauke da sinadaran guba a yankuna da ke hannunsu, wadanda kuma suka janyo mutuwar mutane da dama, ciki harda mata da kananan yara yayin da suke yin barci.
Akwai dai na'urorin bidiyon da a ka fitar, wadanda ke nuna ma'aikatan lafiya na jinyar mutanen da babu wani rauni a jikinsu, kana ba sa zubar da jini. Sai dai kuma, kwararru a harkar lafiya ba su tabbatar da sahihancin lamarin ba.
Jakadiyar kasar Argentina a Majalisar Dinkin Duniya, wadda a yanzu ke shugabantar kwamitin sulhun majalisar, Mario Christina Perceva, ta bukaci samun karin bayani dangane da zargin, da kuma gudanar da cikakken bincike. Ko da shike kafofin yada labaran gwamnatin Siriya, sun yi na'am da batun fada a kusa da birnin Damascus, amma sun karyata zargin yin anfani da makamai masu guba.
Wani dan jarida, kana kwararre a harkokin da suka shafi Siriya, mai suna Kurt Pelda , ya ce yana da wuya a tantance sahihancin labarin:
Ya ce " Ina ganin abin da muke da tabbas shi ne cewar, an yi kissan kiyashi a birnin Damascus, kana babu wani rauni ko kuma alamar zubar da jini a gawarwakin. Saboda haka, tabbaci ne na cewar, ba a yi anfani da makaman da aka saba gani ba, wajen kissansu. Sai dai abin da bamu sani ba, shi ne ko guba ce, kuma idan guba ce ta yaya a ka yi anfani da ita, kana wani bangare ne ke da alhakin hakan."
Majalisar Dinkin Dunya dai ta kiyasta cewar, ya zuwa yanzu fiye da mutane dubu 100 ne suka mutu a yakin basasar Siriya, da ya faro tun a cikin watan Maris na shekara ta 2011.
Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu