1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annan ya fara yin sulhu a rikicin siyasar Kenya

January 23, 2008
https://p.dw.com/p/CwJJ

Tsohon babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya na Nairobin babban birni ƙasar Kenya don ganawa da shugaba Mwai Kibaki da jagoran ´yan adawa Raila Odinga. Jim kaɗan bayan isarsa a Nairobi mista Annan ya faɗawa manema labarai cewa zai nima mutanen biyu da su shiga tattaunawa kai tsaye kana kuma su girmama dokar ƙasa. Annan da sauran shugabannin Afirka dake ƙoƙarin yin sulhu suna fatan warware rikicin siyasar kasar da ya fara bayan zaɓen shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Disamba, wanda Odinga da magoya bayansa suka yi zargin an tabƙa magudi.Kimanin mutane 700 aka kashe sannan aka tilastawa wasu dubu 250 barin gidajensu tun bayan bayyana sakamakon zaɓen na ranar 27 ga watan Disamba.