1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Annobar Coronavirus ta jefa jama'a cikin fargabar rasa aiki

Ramatu Garba Baba
February 11, 2020

Gwamnatin kasar Chaina ta ce mutum kimanin 108 ne suka mutu a wannan Talata a sakamakon cutar Coronavirus baya ga wasu akalla dubu arba'in da takwas da ke kwance a asibiti.

https://p.dw.com/p/3XZw5
China Corona-Krankenhaus in Wuhan
Hoto: Imago-Images/Xinhua/Xiong Qi

A yayin da gwamnatin kasar Thailand ke cewa an kuma gano wani mutum guda da ya kamu da cutar Coronavirus a wannan talata din nan, gwamnatin Chaina ta ce adadin mutanen da cutar ta kashe ya haura zuwa dubu daya, wanda ke nufin mutum dari da takwas Coronavirus ta halaka a wannan Talata a yayin da mutum fiye da dubu arba'in ke jinyar cutar mai kama numfashi.

Kawo yanzu, cutar ta bulla a wasu kasashen duniya ashirin da hudu. Hukumar Lafiya na ci gaba da yin kira na a dauki matakin gaggawa don dakile cutar.

Yanzu haka jama'ar kasar China na cike da fargabar rasa aikin yi duk da tabbacin da shugaba Xi Jinping ya bayar na hana korar ma'aikata. Annobar ta haifar da munmunar nakassu ga tattalin arzikin kasar inda ta yi sanadiyyar mummunar faduwar hannayen jarin, wanda ba a ta taba gani ba a cikin shekara hudu.