1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Antony Blinken ya gana da shugabannin yankin Gulf

Binta Aliyu Zurmi
June 7, 2023

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gana da wasu shugabannin kasashen yankin Gulf a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4SJky
Saudi Arabien | Antony Blinken in Riad
Hoto: Ahmed Yosri/AP/picture alliance

Kafin halartar taron ministocin yankin na Gulf, Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gana da ministan harkokin kasashen ketare na Saudiyya, Yarima Salman bin Farhan.

Daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna, har da hada karfi da karfe domin yakar ta'addanci gami da kawo karshen rikicin kasashen Yemen da Sudan.

Ko a jiya ma Antony Blinken ya gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman inda suka tattauna batun matsalar take hakkin dan Adam da kuma yiwuwar kyautata tsamin dangantaka tsakanin Saudiyya da Isra'ila.

Ziyarar babban jami'in na Amirka da ke zama irinta ta farko tun bayan Saudiyya ta maida alakarta da Iran, wacce kasahen yamma suka raba gari da ita a kan makamaman nukiliya da suke zargin tana kerawa a asirce.