Arangama tsakanin dakarunTurkiyya da 'yan awaren PKK
June 19, 2012An gwabza wani ƙazamin faɗa, tsakanin dakarun gwamnatin Turkiyya, da sojojin aware na ƙurdawa, a yankin Hakkari dake kan iyakokin Turkiyya da Iraki.
Wannan shine faɗa mafi muni da ɓangarorin biyu suka gawbaza tun farkon shekara da muke ciki.
Sojoji Takwas na gwamnatin Ankara sun rasa rayuka, sannan kusan 20 suka ji raunuka, a yayin da ƙurdawan suka yi asara dakaru 10.
Wannan faɗa ya ɓarke bayan da dakarun awaren PKK, suka kaiwa wasu sojojin gwamnati farmaki, kamin daga bisani su arce cikin tsaunukan yankin Kurdistan.
Daga lokacin da PKK ta ɗauki makamai a Turkiyya a shekara 1984 zuwa yanzu, aƙalla mutane dubu 40 suka rasa rayuka a cikin arangama da dakarun gwamnati.
Turkiyya da Amurika da kuma ƙasashen ƙungiyar Tarayya Turai ,na ɗaukar ƙungiyar aware ta PKK a matsayin ƙungiyar ta'adanci.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu