1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Artabu da 'yan sandan Israila a masallacin Al Aqsa

Mohammad Nasiru Awal
May 21, 2021

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fuskanci kalubale bayan da aka yi arangama tsakanin Falasdinawa da ke zanga-zanga da 'yan sandan Isra'ila lokacin sallar Jumma'a a harabar masallacin Al-Aqsa da ke birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/3tnUB
Israel Ausschreitungen Al-Aqsa Moschee in Jerusalem
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kasashe duniya ke maraba da kuma fatan dorewar yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Isra'ila da Hamas bayan kwashe tsawon kwanaki 11 ana barin wuta tsakanin sannan biyu.

Rahotannin daga birnin Kudus na cewa 'yan sandar Isra'ila sun harba gurneti da hayaki mai sa kwalla yayin da Falasdinawa suka yi ta jifansu da duwatsu bayan da daruruwan Falasdinawa suka shiga jerin masu bikin kawo karshen rikicin suna dauke da tutocin Falasdinu da na Hamas suna kuma rera wakokin kungiyar da ke iko a Gaza. Ba a dai san bangaren da ya fara rikicin na wannan Jumma'ar ba, sai dai baki daya ana mutunta shirin tsagaita bude wutar, wanda shugaban Amirka Joe Biden ya ce yanzu suna da kyakkyawar damar samun ci-gaba, kuma zai yi duk iya kokarinsa na ganin an yi aiki don cimma zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Israel Ausschreitungen Al-Aqsa Moschee in Jerusalem
Hoto: Ahmad Gharabli/AFP/Getty Images

Shi ma a nasa bangare ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, wanda a tsakiyar wannan makon ya yi tattakin zuwa yankin inda ya gana da hukumomin Isra'ila da na Falasdinu don neman mafita daga rikicin ya ce hankalinsa ya kwanta ganin an amince da shirin dakatar da yakin.

"Hankalina ya kwanta yanzu da aka dakatar da bude wuta a Isra'Ila da Gaza. Tun a lokacin tattaunawar da na yi a Isra'ila mun ga wannan alama. Wannan na zama muhimmiyar madogarar tabbatar da cewa ba a sake samun wani tashin hankali ba. Aiki na gaba yanzu shi ne magance musabbabin rikicin domin samun maslaha ga rikicin yankin Gabas ta Tsakiya."

Israel Ausschreitungen Al-Aqsa Moschee in Jerusalem
Hoto: Ammar Awad/REUTERS
Israel Ausschreitungen Al-Aqsa Moschee in Jerusalem
Hoto: Mahmoud Illean/AP/picture alliance

Ita ma kasar Sin wato China ta yi maraba da tsagaita wutar tana mai nuna fatan kawo karshen rikicin a kuma koma tattauna batun zaman lafiya. Gwamnatin a birnin Beijing ta ce dole ne gamaiyar kasa da kasa ta ba da gagarumin tallafi ga yankin, inda tuni Chinar ta ce ta ware dala miliyan daya na taimakon gaggawa da wani dala miliyan daya kuma ga aikin jin-kai da Majalisar Dinkin Duniya ke yi wa al'ummar Falasdinu. Zaho Lijian shi ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen China.
"China ta yi maraba da tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu na Falasdinu da Isra'ila, muna kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta duba batun koma kan teburin sulhu domin cimma maslaha ta dindindin ga batun Falasdinu a kan muradin kafa kasashe biyu makwabtan juna."

A wani mataki na gaggawa Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a aika tare kuma da ba da damar shiga da magunguna da sauran kayayyakin jinya a Zirin Gaza, daidai lokacin da likitoci da ma'aikatan jinya ke aiki ba dare ba rana don kula da wadanda suka samu raunuka lokacin barin wutar tsakanin Isra'ila da Hamas. A nata bangaren kungiyar agaji ta Red Cross a ta bakin daraktanta a Gabas ta Tsakiya, Fabrizio Carbon ya ce barnar da aka yi a tsukin kwana 11 ba kadan ba ne.

"Yau ya kamata hankali ya karkata ga sake gina yankin da farfado da shi. Abin bakin ciki ne yadda za a dauki tsawon shekaru kafin a iya sake gina yankin saboba barnar da aka yi ba kadan ba ce."

Isra'ila ta rasa mutum 12 sannan 335 sun ji rauni a yayin da Falasdinawa a Gaza suka rasa mutum 232 sannan 1900 suka samu rauni a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta Gaza.