1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Aski ya zo gaban goshi a zaben shugaban Amurka

November 5, 2024

An zo gabar karshe ta kammala yakin neman zaben shugaban kasar Amurka da za a bude rumfunan kada kuri'a a gobe Talata, 5 ga watan Nuwamba 2024.

https://p.dw.com/p/4mb9B
Fadar mulkin Amurka ta White House da ke gundumar Columbia a birnin Washigton DC
Fadar mulkin Amurka ta White House da ke gundumar Columbia a birnin Washigton DC Hoto: Dean Pictures/IMAGO

'Yar takarar shugabancin kasar a jam'iyyar Democrats Kamala Harris za ta karkare yakin neman zabenta a Pennsylvania, dake da yawan kuri'un da ke da tasiri a yawan wakilai na musamman da aka fi sani da Electoral College, wadanda su ke tabbatar da nasarar shugaban kasa bayan an kammala kada kuri'a a hukumance.

Karin bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka

A gefe guda, 'dan takara a jam'iyyar Republican Donald Trump na ta kai komo a jihohin uku da suka hadar da North Carolina tare kuma da yada zango har sau biyu a Pennsylvania.

Karin bayani: Kamala Harris na samun goyon bayan 'yan Democrat 

Yakin Gaza da batun bakin haure da dokar zubar da ciki da yakin Ukraine da Rasha da harkokin sauyin yanayi har ma da batun inshorar lafiya na daga cikin muhimman batutuwan da 'yan takarar suka tafka muhawara a kai wajen zawarcin kuri'un Amurkawa.