Najeriya : Kungiyar ASUU ta zarce da yajin aiki
March 14, 2022Wani taron majalisar koli ta kungiyar a Abuja ne ya yanke hukuncin tsawaita yajin aikin da ya share tsawon wata guda ya kuma dakatar da harkokin ilimi a kasar. Kungiyar ASUU na zargin mahukuntan Najeriya da halin ko in kula a cikin jerin alkawuran dake a tsakaninta da bangaren gwamnati tun daga shekarar ta 2009. Duk da cewar Abujar ta yi nisa a kokarin cika alkawarin samar da kudaden farfado da harkokin jami'o'in Najeriya, kuma tuni gwamnati ta ce ta samar da kusan Naira miliyan dubu 92 na alawus ga malaman da sauran 'yan aikin jami'o'i, sun gaza burge malaman da suka share tsawon makonni hudu suna yajin aikin, kuma Farfesa Abdullahi Sule Kano ya ce gwamnati ba ta da niyar ceto ilimi daga barazanar da yake fuskanta
Karin bayani : ASUU ta shiga sabon yajin aiki
"Idan ba a yi yajin aiki ba ba yadda za'a yi gwamnati a karin kanta ta tashi ta ce ta ware kudi ga jami'o'i.Tun da gwamnatin nan ta zo abun da muke gani shi ne yawan kudin da ake sakawa a harkar ilimi ya ragu, sun gwammace su bi shawarar abokan huldarsu da masu yaudararsu cewa za su gyara Najeriya.A tambaya nawa su ka dauka suka ba yan Genco da Disco masu samar da wuta? Nawa ne suka sa a matsayin tallafi ga bankunan da suka rushe don kada su rushe?"
Karin bayani : Karin kudin karatu a jami'o'in Najeriya
Kara tsawon yajin aikin dai na nufin a share wattani uku babu karatu a jami'o'in tarrayar Najeriyar a gaba, abun kuma ke da babbar illa ga makomar ilimi a jam'o'in kasar da ma dubbun-dubatar daliban da ke fatan sauyin rayuwa cikin makarantun, in ji comrade Zakariya'u Sarki jigo a kungiyar dalibai na jami'o'in tarrayar Najeriyar da ke sashen Arewa maso yammacin kasar. " Abu ne da muke kallonsa na maras dadi abu ne da muke kallonsa na maras kishi a ce ba za'a iya samun matsaya ba akan abu mai muhimmanci da ya shafi matasa ba a kasar nan. Abu ne da bama jin dadinsa kwarai da gaske."
Karin bayani : Gwamnati da malaman jami'a takon saka a Najeriya
Kishi a cikin tsarin ilimi ko kuma kokarin biyan bukata dai ana kallon gwagwarmayar ta ceton ilimi da idanu na dora fifita kudi bisa harkar ilimin miliyoyi 'yan Najeriya, kana kuma yajin aikin na zuwa ne a cikin tsakiyar rikicin zamantakewa da matasa suka runguma a kasar. Daga yahoo-yahoo ya zuwa satar al'umma, matasan cikin kasar sun yi nisa a karatun rushewar tarbiya, kana kuma a fadar Adamu garba dake nazari kan harkokin zamantakewa akwai babban hatsari ga makomar matasan Najeriya a wannan yanayin na yajin aikin da malaman makarantun suka shiga. Yajin aikin da ke zama na Uku a karkashin gwamnatin APC dai na iya tasiri har a siyasar kasar da ke dada kamari yanzu.