1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU: Mayakan IS 6,000 za su koma Afirka

Yusuf Bala Nayaya MNA
December 11, 2017

Akwai kimanin mayaka na sakai 6,000 daga kasashen Afirka cikin mayaka 30,000 na kasashen waje da suka shiga rundunar 'yan ta'addar IS.

https://p.dw.com/p/2p7Yr
SDF bei Raqqa
Hoto: Picture alliance/AP Photo/Syrian Democratic Forces

Kimanin mayakan sakai 6,000 ne daga kasashen Afirka wadanda suka tallafawa 'yan kungiyar IS a kasashen Iraki da Siriya ake fargabar za su koma gida kamar yadda babban jami'i a harkar da ta shafi tsaro a Kungiyar AU ya bayyana a ranar Lahadi, inda ya yi gargadi ga kasashen da su zauna cikin sanya idanu kan wadannan masu ikirari na Jihadi da za su kama hanyar komawa kasashensu na asali.

Smail Chergui, kwamishinan zaman lafiya da tsaro a kungiyar ta AU ya ce akwai bukata ta ganin kasashen na Afirka sun rika musayar bayanan sirri a tsakaninsu ta yadda za su lura da shige da fice na mayakan sakan.

A cewar kamfanin dillancin labaran Aljeriya Chergui ya fadi a wajen wani taro a birnin Algiers cewa akwai kimanin mayakan na sakai 6,000 daga kasashen Afirka cikin mayaka 30,000 na kasashen waje da suka shiga rundunar 'yan ta'addar da suka yi fadace-fadace a yankin Gabas ta Tsakiya.