1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta nuna adawa da matakin soja a Zimbabuwe

Gazali Abdou Tasawa
November 16, 2017

Kungiyar Tarayyar Afirka ta AU ta yi tir da Allah wadai da abin da ta kira wani abu mai kama da juyin mulki da sojojin Zimbabuwe suka aiwatar a kasar kana ta yi kira da su mutunta kundin tsarin mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/2nhmA
Porträt - Alpha Conde
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Padilla

A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Laraba Shugaba Alpha Conde  na Guinea wanda ke shugabancin Kungiyar ta AU a yanzu ya yi kira ga sojojin kasar ta Zimbabuwe da su yi biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar da ma dakatar da duk wani matakin da suka dauka ya zuwa yanzu. Rundunar sojin kasar ta Zimbabuwe wacce ta ja daga tare da baza tankokin yaki a wuraren da dama na birnin Harare ta sanar da cewa ba juyin mulki ta yi ba, illa dai tana aikin tsarkake mulkin kasar ne daga miyagun mutanen da ke kewaye da Shugaba Mugabet wanda ke da shekaru 93 a yau a duniya.