Aukuwar sabuwar girgizar ƙasa a Japan
March 16, 2011An samu ƙarin wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki shidda a ma'aunin Richter a gabashin birnin Tokyo inda manyan sorraye suka riƙa girgijewa. Sai dai hukumar binciken yanayi ta ƙasar ta ce babu hatsarin aukuwar wata igiyar ruwa akan wannan girgiza da aka samu. Wata 'yar jarida a birnin Tokiyo ta shaida yadda lamarin ya faru .Ta ce ina zaune a offishina sai na ji kamar ana ƙwonƙwosa mani ƙoffa ko da na rego sai na ga gidaje na yin tankal tankal ama kawo yanzu kuma na tafiya dai dai motoci suna yin zirga zirga kuma babu wata asara da aka samu ko ta rayuka ko ƙadarori.
Sannan a halin da ake ciki hukumomin ƙasar ta Japan sun ce wani gini na fuɗu na tashar makamashin nukiliya na Fukushima ya sake kamawa da wuta kuma hayaƙi ya turniƙe sararin samaniya, kafin daga bisani mintoci talatin wutar ta mutu kamar yadda gwamnati ta shaidawa hukumar samar da makamashi ta duniya IAIE, yayin da aka kwashe ma'aikata daga gurin kafin su ma daga bisani a sake dawo da su.
Wani kakakin gwamnati, Yukio Edano ya bayyana cewa turirin yana raguwa kuma yana ƙaruwa lokaci zuwa lokaci amma ya ce alah-kulli-hali akwai hatsari ga lafiyar jama'a.
Zafin turarin dai kawo yanzu ya sa an dakatar da yunƙurin da ake yi na sanyaya tukanan tashar makamashin nukiliyar ta Fukushima .
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita Mohammad Nasiru Awal