1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayarin Majalisar Dinkin Duniya a Siriya

April 26, 2012

Kasashen ketare na zargin gwamnatin Siriya da kin mutunta alkawuran da ta yi na bada hadin kai ga aiwatar da shirin samar da sulhun Kofi Annan

https://p.dw.com/p/14lIb
Colonel Ahmed Himmiche (front) of Morocco, leader of the first U.N. monitoring team in Syria, and several members of his team leave a hotel in Damascus April 25, 2012, to patrol areas of protests against the regime of Syrian President Bashar al-Assad. REUTERS/Khaled al- Hariri (SYRIA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS)
Hoto: Reuters

Tawagar share fage na masu sanya idon Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, basu da yawan ciyo kan rikicin kamar yadda aka zata tun farko. Bisa dukkan alamu ba zasu iya tabuka komai ba dangane da matakin tsagaita wutar da ya ki aiki, amma kuma a wani abun da ke janyo damuwa, wasu rahotanni sun nunar cewa dakarun gwamnati sun bindige wadansu wakilan birnin Hama da suka gana da tawagar masu sanya idon.

Wakilin kasa da kasa mai shiga tsakanin rikicin na Siriya Kofi Annan yana sa ran al'ummar kasa da kasa zata cigaba da sanya ido kan abunda ke faruwa a Siriya a kuma hanzarta wajen tura tawagar masu sanya ido mai mambobi dari ukun da Kwamitin Sulhu ya amince da su. A hakika mai shiga tsakanin ya san alhakin da ya rataya kan masu sanya idon kamar yadda Ahmad Fawzi mai magana da yawun Kofi Annan ya bayyana:

"Gwamnatin Siriya bata da wani zabi illa ta bar wadannan masu sanya ido, domin da kan su suka amince  da shirin mai kudurori shidda, sun kuma amince da a tura masu tawagan masu sanya ido, muna kuma aiki da su domin tura jami'an, kuma ya kamata su bada tabbacin samar da kariya da kuma izinin zurga-zurga ba tare da matsin lamba ba, haka yarjejeniyar take"

NEW YORK, April 5, 2009 (Xinhua) -- The U.S. Ambassador to the United Nations Susan Rice addresses the media prior to an emergency Security Council meeting called by Japan on April 5, 2009 at UN headquarters in New York after the rocket launch of the Democratic People's Republic of Korea (DPRK). Xinhua /Landov
Jakadar Amurka a MDD Susan RiceHoto: picture alliance / landov

Alkawarin gwamnati na Janye dakarunta

To amma a zahiri ba haka ake gani ba, gwamnatin ta ce ta janye dakarunta da manyan makamai daga biranen kasar amma ko Rasha da ke zaman babbar kawarta bata amince da wannanba, yanzu kuma ga batun tsaron 'yan Siriyan, ganawar da tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da gwamnatin bata bada tabbacin komai ba, mai magana da yawun Anan Fawzi ya yi karin bayani

"Na sami rahotanni daga mutanenmu da ke wurin cewa da zarar masu sanya idon suka tafi, dakarun soji da ma sauran magoya bayan gwamnatin Siriyar kan razana su, ba zamu amince da wannan ko daya, wajibi ne a dakatar da shi cikin gaggawa, shi ya sa mu kan ce yanayin rashin tabas na tsagaita wutan ya kara nuna mahimmancin sake tura wata tawaga kasar cikin gaggawa"  

Dangane da batun tura dakaru masu hulan kwanon mai ruwan bula guda 300 daga Majalisar Dinkin Duniya, tura dakarun farko kawai sai da ya dauki wata guda daga birnin New York, wanda aka ce kudurin kawai na daukar watanni uku

Matsayin "kawayen Siriya" dangane da wannan rikicin

Jakadar Amurka a Majalisar, ta yi kakkausar suka ga rashin amincewar Assad da ya marabci masu sanya idon daga kasashen da shi kansa ya kira kawayen Siriya, wadanda suka hada da Amurka, Burtaniya, Faransa, Saudiyya, Katar da Turkiya. Sune kasanshen da ke adawa da halin gwamnatin Siriyar kuma sun yi barazanar goyon bayan 'yan tawayen idan gwamnatin bata bada hadin kai ba. Wata matsala kuma in ji Timur Goskel wanda ya yi sama da shekaru 20 yana aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon ita ce:

"Suna da rawar takawa mai mahimmanci sosai, sai dai daga karshe abun faragabar shi ne idan har ba'a yi nasara ba, za'a fara baiwa tawagar masu sanya idon laifi kamar yadda aka yi da tawagar sanya idon kungiyar hadin kan Larabawa, kada mu sanya dogon buri, domin na ga kamar muna neman abubuwa da yawa daga wajen wadannan mutane. kasancewarsu a kasar zai iya rage tashe-tashen hankula amma ba zai kasance matakin warware matsalar ba"

In this photo released by the Syrian official news agency SANA, a UN observers vehicle passes under a huge Syrian flag held by Syrian President Bashar Assad supporters during their visit to the pro-Syrian regime neighborhoods, in Homs province, central Syria, on Monday April 23, 2012. United Nations observers monitoring Syria's shaky cease-fire visited a string of rebellious Damascus suburbs Monday, while the European Union looked set to levy new sanctions to increase the pressure on President Bashar Assad's regime. (Foto:SANA/AP/dapd)
Hoto: AP

Kofi Annan ba shi da wani bayani bisa dalilan da suke janyo jinkiri wajen aiwatar da shirin nasa, to sai dai babban ayar tambaya ita ce kusan dakarun wanzar da zaman lafiya dubu 15 suka taimaka wajen tabbatar da tsaro a kasar Lebanon, makociyar Siriya, to amma al'ummar Siriyar, ta ninka na Lebanon har sau shidda, sojoji saboda haka, sojoji dari uku zasu iya shawo kan wannan rikicin?

Mawallafa: Leidholt Ulrich/Pinado Abdu Waba
Edita:         Mohammed Awal Balarabe

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani