1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan tarzoma a Najeriya da rundunar ko takwana a Afirka

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2015

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan ta'addanci a Afirka da badakalar amfani da magunguna kara kuzari a wasannin motsa jiki.

https://p.dw.com/p/1H9aD
Anschlag von Boko Haram in Yola, Nigeria
Hoto: Reuters/Stringer

A wannan makon jaridun gaba ki dayansu sun mayar da hankali ne kan hare-haren ta'addancin da suka girgiza birnin Paris na kasar Faransa, amma duk da haka wasunsu sun leka nahiyarmu ta Afirka kamar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta yi tsokaci kan wani harin ta'addancin a Tarayyar Najeriya.

Ta ce garin Yola na jihar Adamawa ya shiga wani yanayi na rashin tsaro, inda mutane fiye da 30 suka mutu sannan da dama suka jikata a wani hari da aka kai a wata kasuwa da yammacin ranar Talata. Jaridar ta ce 'yan tarzomar sun zabi wurin da suka kai harin ne da kuma lokacin aiwatar da harin domin samun mutane da yawa da abin zai iya shafa. An samu fashewar bam din ne da maraice a daidai lokacin da mutane ke hada-hadar komawa gida. Ko da yake ba wanda ya yi ikirarin kai harin amma yana da alamun aikin kungiyar Boko Haram. Da jimawa dai Yola da ke zama shelkwatar jihar Adamawa, ta kasance wani wuri mai kwanciyar hankali inda ma mazauna garin ke alfahari da zaman lafiya da fahimtar juna da ke tsakanin mabiya addinai dabam-dabam. Harin na ranar Talata shi ne na hudu a cikin wannan shekara.

Rashin kudi ga rundunar ko takwana ta Afirka

Har yanzu dai muna kan batun na tarzoma inda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce rundunonin soji a kasashen Afirka na fama da karancin kudi amma duk haka an dora musu nauyin yakar kungiyoyin tarzoma na masu kishin addini.

Mali Geiselnahme Hotel in Bamako
Hoto: H. Kouyate/AFP/Getty Images

Ta ce "Amani" kalma ce ta harshen Suwahili da ke nufin zaman lafiya, kuma "Amani Africa 2" shi ne sunan wata rundunar sojoji 5400 daga kasashen Afirka fiye da 12 da za su kasance cikin shirin ko takwana, da kuma za a iya girke su a wani yanki na Afirka da rikici ya barke. Wannan runduna ta kungiyar Tarayyar Afirka za ta kasance wata maslaha ga matsalolin nahiyar. Sai dai kamar yadda aka saba gani a wannan nahiya, a wannan karo ma akwai makeken gibi tsakanin magana ta fatar baka da kuma gani a aikace. Babbar matsala a nan ita ce ta kudi. To sai dai ana fata kasashen Turai za su taimaka domin matsalar rashin tsaro ta zama ruwan dare gama duniya.

Sama da fadi da kudin tallafi ga wasan motsa jiki

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi kan wasannin motsa jiki.

China Leichtathletik WM in Peking - Männer 1500m - Asbel Kiprop
Batun amfani da magungunan kara kuzari ya yi yawa a fannin wasan tsereHoto: Getty Images/A. Lyons

Ta ce bayan badakalar amfani da haramtattun magungunan kara kuzari da ta shafi 'yan tsere kasar Kenya, yanzu shugabannin hukumar wasannin motsa jiki ta kasar ne ake zargi da yin almundahana da kudi kimanin dala dubu 700. Mutanen da abin ya shafa sun hada da David Okeyo da ke zama memba na hukumar kula da wasan tsere ta duniya wato IAAF. Yanzu haka dai kwamitin da'a na hukumar ya fara gudanar da bincike. Ana zargin Okeyo da ya kwashe sama da shekaru 25 a sahun gaba na jagororin hukumar wasannin motsa jikin kasar Kenya, da wasu mutane biyu da laifin karkata akalar kudaden tallafa wa wasanni da suka kai dala dubu 700.