Azumin Ramadana cikin annobar Coronavirus
Addinin Kirista ko Musulunci: Imani ne ke taimakawa a yanayi mai tsauri. Amma idan Masallatai suna kulle, wurin ibada ya daina zama wajen haduwa? Musulmi sun san yadda za su taimaki juna a lokacin azumin watan Ramadana.
Saudiyya: Sai masu shara ba kowa
Zai yi wuya ka san abin da zai faru idan akwai mutanen da suka saba taruwa a dakin Ka'aba da ke birnin Makka. Annobar cutar Coronavirus ta takaita mutane da suke wannan aiki. Akwai tsirarun mabiya da suka zo babban Masallacin a farkon watan Ramadan. Galibin mutanen da suke cikin hoton masu shara ne, wadanda yanzu aikin da suke yi yake da muhimmanci.
Siri Lanka: Azumi duk da annoba
A karkashin matakan kasashen Turai, wannan taruwar iyalin a birnin Malwana na Siri Lanka, ba zai yiwu ba saboda annobar cutar Coronavirus. Mutane ba sa nesa da juna kuma suna kokarin buda-baki na azumin watan Ramadana. Suna addu'ar karshe kafin buda-bakin.
Isra'ila: A kan dardumai nesa da juna
A Isra'ila, ana bin matakan yaki da cutar Coronavirus sau da kafa. Falasdinawan da ke nan Jaffa sun bi matakan. Zama a wurin da ake ajiye motoci ya samar da filin da ake bukata domin yin nesa da juna.
Indonesiya: Salla da abin rufe baki da Internet
A Jakarta babban birnin Indonesiya wayoyin hannu da internet sun zama ruwan dare, hakan ya taimaki wani limami mai suna Bambang Suprianto. Yana karanta al-Kur'ani da addu'a ta Internet daga Masallaci ta kafofin sada zumunta. Suprianto ya zama abun koyi, saboda yana karatun sanye da takunkumin rufe fuska na kariya.
Amirka: A cikin wasiku masu yawa
Musulman da suke Daerborn da ke Michigan ba su manta da azumin watan Ramadana ba. Masu aiki a Masalalci sun bayyana fara azumin a cikin wasikun da suka rabawa mabiya, inda aka rubuta: "Ramadan Kareem."
Siri Lanka: Kallon sararin samaniya
Za ka iya yin salla kai kadai- Ko da Masallatai na cika a lokacin azumin watan Ramadana. Amma idan kai kadai ne, mutum zai iya shimfida darduma a kan rufin gida a birnin Colombo na Siri Lanka ya hango sararin samaniya. Wannan yaron ya daga hannunsa sama yana kallon sama yana addu'a, lokacin da yana jiran lokacin da za a sha ruwa domin kammala azuminsa na wannan rana.
Jamus: Bidiyo daga Masallaci mai kyau
Mutane da dama na cewa an bar Jamus a baya idan ana maganar Internet. Ko haka ne: Benjamin Idris limanin cibiyar Islama da ke garin Penberg na jihar Bavariya, yana amfani da wayar salula wajen isar da karatunsa na al-Kur'ani ta Internet. Cikin wannan hoto za a gane dalilin bai wa taswirar Masallacin lambar yabo, lokacin da aka bude shi a shekara ta 2005.
Turkiyya: Yana kyalkyali amma ba kowa a ciki
Ba kawai wannan husumiyar ta Galata da ke birnin Santanbul ce babu kowa ba a wannan yammaci. Mahukuntan kasar sun umurci a rufe daukacin Masallatan da ke kasar Turkiyya lokacin azumin watan Ramadan. Ita ma Turkiyya tana yaki da cutar COVID-19. Haka kuma wannan hoton mai kyalkyali, na nuna yadda ake kokarin dakile komai.
Nepal: Kiran salla
Abubuwa kalilan ke aiki kullum a Kathmandu babban birnin Nepal. A ranar farko da aka fara azumi, an kira salla. Duk da annobar cutar Coronavirus, ana jin kiran sallah a duk lokutan salla a tsawon rana kamar yadda aka saba.
Singapore: Dandalin baje koli ya taimaka
Ginin zamani da aka yi domin baje kolin kayayyaki dabam-dabam a Singapore. Harkokin tattalin arziki sun tsaya a duniya baki daya, kuma babu wata dama nan kusa na yin baje kolin wani abu. Ginin ya zama wajen da ake kula da masu dauke da cutar COVID-19 da kuma yin salla lokacin azumin watan Ramadana.
Watan Ramadana lokacin azumin Musulmi. A wannan shekarar, an fara ranar 23 ga watan Afrilun da muke ciki kuma za a kammala a ranar 23 ga watan Mayu mai zuwa. Batu ne na abin da Musulmi suka yi imani da shi ko da akwai Coronavirus ko babu.