1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba´a samu wani ci-gaba ba a taron kan shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa

December 21, 2006
https://p.dw.com/p/BuWl

Mahalarta taron kasashe 6 game da shirin nukiliyar KTA sun ce har yanzu ba´a samu wani ci-gaba na a zo a gani a tattaunawar da ake yi a birnin Beijing ba. A dai halin yanzu gwamnati a birnin Pyongyang ta ba da jerin bukatu da ta ce dole a biya mata su kafin ta fara duba yiwuwar kwance damara. Daga cikin bukatun kuwa har da nema a kawo karshen takunkuman kudi da Amirka ta kakaba mata. Wakilin Amirka a taron Christopher Hill ya nuna shakkun cewa ba za´a kai ga wani tudun dafawa ba a cikin wannan mako. Shi kuwa wakilin Japan Kenichiro Sasae cewa yayi tattaunawar ta yini 4 ba ta cimma wani ci-gaba ba saboda kin da KTA ta yi na sassautowa daga bukatun ta.