1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnonin Najeriya sun mamaye siyasa

January 17, 2022

A yayin da gwamnonin APC ke neman kashe rikici tare da tabbatar da babban zaben jam'iyyar, takwarorinsu na PDP na nazarin dabarun iya kwace goruba a hannun kuturu.

https://p.dw.com/p/45emP
Nigeria Flagge
Hoto: Leonid Altman/Zoonar/picture alliance

A wani abun da ke tabbabatar da karuwar babakeren gwamnoni a cikin fagen siyasar tarrayar Najeriya, gwamnonin APC da 'yan uwansu na jam'iyyar PDP ta adawa dai sun bude mako da kokari na tabbatar da babakerensu cikin harkoki na siyasa ta kasar.

Kama daga APC mai mulki ya zuwa PDP ta adawa dai gwamnoni a cikin jam'iyyun tarrayar Najeriya guda biyu dai na maida hankali a kokarin fafatawa da kila ma kwace goruba a hannun kuturu a siyasa ta kasar.

Wata mata na kada kuri'a
Wata mata na kada kuri'artaHoto: AP

Batun siyasa ta kasar da uwa uba zabe na shugaban tarrayar Najeriyar ne dai ke dauka ta hankalin gwamnonin da sannu a hankali ke kara fitowa fili a matsayin gogarma a siyasar mai tasiri.

Tarukan kuma da suka dauki hankali na masu siyasa da ma ragowar al'umma tarrayar Najeriyar da ke kallo na zabukan badi da alamu na damuwa. To sai dai kuma babakeren gwamnonin a kokari na juya akala ta siyasar tarayyar Najeriyar dai na kara fitowa fili da irin girman rikicin da ke fagen siyasar kasar.

Tuni dai dama su ka yi bakin jini wajen nadi da sauke da dama walau a mataki na shugabancin jam'iyyu a jihar, abun kuma da ya kai ga haihuwa ta bangarori da yawa na shugabancin jam'iyyun a jihohin, ko bayan raba kan 'yan jam'iyyun bisa batu na fidda gwanayen jam'iyyun a zabuka na shugaban kasar a shekarar badi.

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Masu kada kuri'u a zaben NajeriyaHoto: DW/Gänsler

Komawa ga mai duka ko dabarar cikin gida dai, kusan biyu a cikin uku na gwamnonin tarrayar Najeriya 36 dai na cikin wa'adin mulki na biyu. Abun kuma da ke nufin dagun hakarkari a neman cika buri na siyasar ko kuma komawa ga rabbana a cikin neman mafita ta rayuwar bayan mulki maras tabbas.

Iko da kudi ne dai a fadar Faruk BB Faruk da ke sharhi bisa siyasa ta kasar shi ya baiwa gwamnonin babakere a cikin fagen siyasar tarayyar Najeriyar ya kuma dora siyasa ta kasar bisa tsari mara tabbas .