Babban fatan kafa gwamnati a Jamus
January 21, 2018Hakan dai ya biyo bayan kar ruwa rana da aka yi tsakanin yayan jam'iyar kafin su amince da shiga tattaunawa tare da shugabar gwamnati Angela Merkel, don duba yiwuwar kafa gwamnatin hadaka. Sai dai wannan batun na shiga gwamnati yana tattare da rudani mai yawa hatta a cikin jam'iyar ta SPD, hakan kuwa ta bayyana a bisa yadda sakamkon kada kuri'ar ya nuna cewa, an amince da fara tattaunawar shiga gwamnatin ne bisa karamin rinjaye. Daga cikin 'yan jam'iyyar 642 wadanda suka hallarci taron, mutane 362 ne suka kada kuriyar yin na'am, wato kusan rabinsu duk sunki amincewa da shiga gwamnatin. Yanzu dai watanni hudu da yin zabe a kasar Jamus, amma ba a samu nasarar kafa gwamnati ba, bisa asaran kuri'un da jam'iyar Angela Merkel ta samu, yayinda ita kuwa jam'iyar SPD, sakamakon zaben na watan Satumba shi ne mafi muni gareta tun cikin shekaru 75 biyar da suka gabata. Wannan shi ne dalilin da yasa magoya bayan jam'iyar suka yi ta kiran kada a shiga gwamnati, a zama bangaren adawa ko hakan ya Allah ya dawo da mutuncin jam'iyar a idanun Jamsuwa. Bisa wannan kada kuri'ar ana saran ba bata lokaci za a share fagen fara tattauna yadda za a kafa gwamnatin hadaka, tsakanin jam'iyar CDU ta Angela Merkel da SPD wace ita ce jam'iyya ta biyu mafi girma, kana mafi tsufa a kasar ta Jamus.