1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China: Sabon ministan harkokin waje na ziyara a Afirka

January 10, 2023

Sabon ministan harkokin wajen China Qin Gang ya fara aikinsa da wata ziyara ta musamman a kasashen Afirka guda biyar. Ziyarar ta kwanaki bakwai na da nufin kara karfin dangantaka a tsakanin Chinan da wadannan kasashen.

https://p.dw.com/p/4Lxpa
Hoto: Kyodo News/IMAGO

Kasashen da babban jami'in diflomassiyar ke ziyarta sun hada da Habasha da Gabon da Angola da Benin da kuma Masar. A ranar 30 ga watan Disamba hukumomin Beijing suka sanar da nada Mr. Gang a wannan mukami. Ya ce fara aikin nasa da ziyarar na nuna irin muhimmancin da China ta bai wa huldar da ke tsakaninta da Afirka.

A cikin shekaru 30 da suka gabata sauran wadanda suka rike mukamin ministan harkokin wajen China dai na fara ziyartar kasashen Afirka a duk farkon sabuwar shekara. Wannan dabara na zuwa ne a yayin da China da Amirka ke ci gaba da gwada-kwanji wajen samun tasiri a nahiyar ta Afirka.