1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taro kan asusun kare muhalli a Berlin

Mohammad Nasiru AwalNovember 20, 2014

Kasashe na tattaunawa game da karo-karon kudi ga wani asusun kare muhalli a duniya.

https://p.dw.com/p/1Dqgb
Green Climate Fund Konferenz in Berlin 20.11.2014
Hoto: AFP/Getty Images/O. Andersen

Wakilai daga kasashe 20 sun fara tattaunawa a birnin Berlin na nan Jamus game da wani asusun tallafa wa aikin kare muhalli. Manufa ita ce sama wa asusun kudi dala miliyan dubu 10, kamar yadda aka amince a wani babban taron Majalisar Dinkin Duniya kan muhalli da ya gudana a birnin Cancun na kasar Mexiko a shekarar 2010. Za a yi amfani da kudaden wajen taimaka wa kasashe masu tasowa samun kandagarkin ambaliyar ruwa da kare gandun daji tare kuma da fadada fasahar sabunta makamashi. Ya zuwa yanzu an tara wa asusun kudi dala miliyan dubu 7.5. Kasar Amirka wadda za ta ba da gudunmawa mafi yawa ta alkawarta dala miliyan dubu uku yayin da Jamus ta ba da Euro miliyan 750.