Babban taron Africa Lumana a Niger
November 13, 2010Jam'iyar MODEEM Africa Lumana ta Niger ta gudanar da babban taronta a birnin Yamai a wannan asabar. Lamarin da ya ba ta damar fit da gwanin da zai tsaya mata takara a zaɓen shugaban ƙasa na shekara mai zuwa. Tsohon firaministan ƙasar wato Hamma Amadou ne jam'iyar ta Lumana ta tsayar ƙarƙashin tutarta kamar yadda aka kyautata zato tun da farko. Hamma ya ce ina da gogewa da zai iya ba shi damar kai labari a zaɓen na baɗi.
Ita dai MODEM Africa Lamuna ita ce jam'iya ta biyar da ta fitar da ɗan takara a jamhuriyar ta Niger baya ga MNS Nasara, da UDR Tabbas, da Tsintsiya, da kuma PNDS tarayya, Hakazalika mace guda wata Mariyama Bayar Damace ta bayyana kanta a matsayin 'yar takara mai zaman kanta.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita Abdullahi Tanko Bala