1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ciyar da nahiyar Afirka gaba a Japan

Mohammad Nasiru Awal LMJ
August 28, 2019

Taron na bana shi ne karo na bakwai tun bayan kaddamar da shi a shekara ta 2016 a birnin Nairobin kasar Kenya.

https://p.dw.com/p/3OdPM
Kenia Internationale Tokio-Konferenz für Afrikanische Entwicklung
Hoto: Reuters/T. Mukoya

A wannan Laraba shugabannin kasashen Afirka da kungiyoyin kasa da kasa sun hallara a birnin Yokohama na kasar Japan don gudanar da babban taron Tokyo na ciyar da nahiyar Afirka gaba da ake wa lakabi da TICAD.

Firaministan Japan Shinzo Abe da ya yi jawabi a gaban mahalarta taron da suka hada har da wakilai na Majalisar Dinkin Duniya da na Bankin Duniya ya jaddada muhimancin magance matsalolin dumamar yanayi da da bukatar samun fasahohi na kirkire-kirkire.

Tuni dai kasar Japan ta yi alkwarin zuba jari mai yawan gaske a nahiyar Afirka don taimaka mata wajen gogayya da sauran nahiyoyi na duniya.

Taron na bana shi ne karo na bakwai tun bayan kaddamar da shi a shekar 2016 a birnin Nairobin kasar Kenya.