1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babbar barazanar yunwa a Sudan ta Kudu

Salissou Boukari
February 26, 2018

Fiye da rabin al'ummar kasar Sudan ta Kudu na fuskantar babban kalubale na matsananciyar yunwa, kaman yadda wani rahoton da wasu kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya guda uku suka wallafa ya yi nuni.

https://p.dw.com/p/2tN9F
Südsudan Hunger Symbolbild
Matsalar yunwa a Sudan ta KuduHoto: Getty Images/AFP/A. Gonzales Farran

A watan Janairu da ya gabata mutane miliyan 5,3 kwatankwacin kashi 48 na al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu ne ke cikin hali na karancin abinci, wanda yanayin matsalar a yanzu ya kai kololuwa. Wannan adadi dai ya karu da kashi 40 cikin 100 a shekara guda kamar yadda kungiyoyin na Majalisar Dinkin Duniya, irin su asusun kula da kananan yara na UNICEF, da  asusun kula da harkokin Noma da yawaitar abinci na FAO, da kuma tsarin abinci na duniya PAM suka bayyana a cikin rahoton da suka fitar.

A shekara ta 2017 Sudan ta Kudu ta fuskanci matsalolin yunwa na tsawon watanni hudu daga watan Febrairu zuwa Watan Juni, kuma matsalar da ta shafi mutane kimanin dubu 100 a yankin Leer da Mayendit da ke Arewacin kasar. Sai dai an samu saukin lamarin a wancan lokaci sakamakon yawaita kai kayan agaji da akayi, amma kuma duk da haka matsalar da ake fuskanta a yanzu haka ta fice misali.