1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu tabbas ko Koriya Ta Arewa ta yi gwajin makamin nukiliya

October 11, 2006
https://p.dw.com/p/BugD

Jakadun manyan wakilai 5 a kwamitin sulhun MDD da na Japan sun kasa cimma daidaito game da yiwuwar sanyawa kasar KTA takunkumi. A saboda haka sun dage zaman shawarwarin da suke yi har zuwa wani lokaci yau laraba. Jakadan Japan a MDD wanda kuma shine shugaban kwamitin sulhu a yanzu, Kenzo Oshima ya ce har yanzu akwai banbance banbance ra´ayi a tsakanin wakilan kwamitin sulhun dake birnin New York. A kuma halin da ake ciki Amirka ta yi maraba da shirin da China ta nuna na goyon bayan sanyawa KTA takunkumi ko da kayyadadde ne. Gwamnatin Beijing ce babbar kawar hukumomin birnin Pyongyang. Har dai halin nan da ake ciki ma´aikatar harkokin wajen Amirka ta ce ba bu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin da KTA ta yi na yin gwajin makamin nukiliyar a ranar litinin.