1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bahasi kan harin ta'addanci a London

October 11, 2010

Bayan shekaru biyar ana cece kuce kan harin bama bamai da aka kai a birnin London, yau an fara yin bahasi kan rawar da jami'an tsaro suka taka.

https://p.dw.com/p/PbJB
'Yan sanda suna bincike bayan harinHoto: AP

A birnin London yau ne aka fara jin bahasi kan harin ta'addanci da aka kai birnin shekaru biyar da suka gabata. Ana gudanar da bahasin ne domin dubu ko da akwai matakan da ya kamata hukumomin tsaro na 'yan sanda da jami'an leƙen asiri su ɗauka, wanda da ya hana kai harin. Bahasin ya biyo neman da iyalan waɗanda harin ya shafa suka nemi a yi hakan. Wannan dai shi ne karo na farko da za'a gudanar da jin bahasi a bainal jama'a tun bayan kai harin na ranar bakwai ga watan Yulin shekara ta 2005. Aƙalla mutane 52 suka rasu a harin na birnin London.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal