Bala'in girgizar ƙasa a Japan
July 10, 2011An samu wata girgizar ƙasa mai kama da tsunami a gaɓar tekun ƙasar Japan. Girgizar ƙasar wadda ta kai matsayin na 7.1 akan ma'auni ta faru ne a yankin Pasifik kuma ta girgiza yankin arewa maso gabashin ƙasar ta Japan. Hukumomin kula da yanayin karkashin ƙasa a ƙasar suka ce tsawon igiyar tsunamin ya kai santimita 10. A ƙasar ta Japan hukumomi sun bai wa yankin da aka yi wa mummunan girgizar ƙasa, wani gajeren gargaɗin yiwuwar samun tsunamin. Girgizar ƙasar da aka yi a watan Maris ta haddasa matsalar makamashin nukiliya a ƙasar ta Japan, kana ta yi sanadiyar mutuwar kimanin mutane dubu 21. A yau 10 ga watan Juli an fitar da ma'aikata daga tashar nukiliyar Fukushima wadda ke a tazarar kilo mita 250 daga inda aka yi girgizar ƙasar. Ba'a dai ba da rahoton samun rauni ko ɓarna ba kawo yanzu.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas